Manyan Dilolin siminti na Kasar nan sunyi martani game da rage farashin da kamfanin BUA yayi


Manyan dilolin siminti a kasar nan sun fara maida martani kan sanarwar kamfanin BUA na rage farashin simintin zuwa naira 3500 a makon nan.

A tattaunawarsu da Premier Radio, wasu daga cikin manyan dilolin Simintin a nan Kano da Jihar Katsina sun ce har yanzu alโ€™umma basu fahimci abinda ragin ke nufi ba, suka ce 3500 da kamfanin ya bayyana, farashin kamfani ne kawai, amma bayan nan akwai kudin dako mai dan karan tsada da suke biya domin kai simintin jihohin su, wanda hakan kan sa farashin ya tashi.

Haka zalika yan kasuwar sun bada shawarar cewa in har kamfanin da gaske yake yi, to ya tabbatar simintin ya kai ga dilolin har jihohin su a wannan farashi na 3500, wato dai motocin kamfanin su dinga kai simintin kyauta, hakan ne kadai zai sanya talaka yaga saukin a fili.

Kafin yanzu dai kamfanin na BUA na ta shan addua da samun yabo daga alummar kasar nan. Kan wanna naimijin kokari da aake gani yayi a wannan lokaci da jamaa ke fama da matsin tatatali arziki.

Koda muka tuntubi guda cikin shugabanin kamfanin na Bua ya ce bashi da hurumin yin magana a yanzu sai dai nan gaba idan ya samu izinin yin magana.

Comments

Popular posts from this blog

BIDIYO: Yadda aka Gudanar da Gasan Lashe Hammata na Wannan shekaran

Ina maza masu karamin mazakunta Gama hanyar dazaki maida gabanku yazam kato๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

"Masha Allah" Mawakin Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinawa

Wata Budurwa ta rasa ranta tana tsaka da saduwa da Saurayinta, hakan yafarune yayin gwajin maganin karfin maza

An karrama mutumin da bai taba shiga aji ba da matakin digiri (Dr) Bayan ya kirkiri risho mai amfani da ruwa Tareda janareto - Abis Fulani News