"Masha Allah" Mawakin Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinawa


Mawaki Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinawa

Shahararren mawaki kuma jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya ziyarci shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.

Lilin Baba ya ziyarci Sheikh Gumi ne domin bayar da gudunmawarsa ga al’ummar Falasdinawa wadanda ke fama da yaki.

Mawakin ya ba shehin malamin N500,000 domin a saka a cikin asusun banki wanda za a tura don taimakawa mutanen Falasdinu yayin su ke cikin wani yanayi na zalunci daga Isra’ila.

Post a Comment

0 Comments