Jami'ar jihar Gombe ta karrama dan Najeriya mai kirkiran abubuwa, Injiniya Hadi Usman da digirgir a bangaren kimiyya.
A cewar babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara ta musamman kan harkokin labarai, Safianu Danladi Mairiga a dandalin X, an bai wa Usman shaidar digiri a bikin yaye dalibai na jami'ar jihar Gombe da aka kammala kwanan nan.
Legit Hausa ta rahoto cewa Usman ya kirkiri risho mai amfani da ruwa.
Sauran abubuwan da mutumin mai tarin baiwa ya kirkira sun hada da gidan radiyo, jirgi mai saukar ungulu wanda ke aiki da injin din Vespa da wayar hannu.
Danladi ya bayyana cewa Usman ya kuma kera wani janareto wanda baya aiki da fetur amma kuma bai yi ilimin boko ba.
Ya kara da cewar mutumin haifaffen gudunmar Jekadafari da ke karamar hukumar Goimbe, jihar Gombe ya haddace Al-Qur'ani mai girma tun yana da shekaru 12 a duniya.
Danladi ya yada hoton Usman a zaune yayin da yake sanye da kayan karramarsa. Kalli wallafar Safiyanu a kasa:
Comments
Post a Comment