Bani na kashe Marigayi Nafi’u ba - Chuchu
Matar auren nan Hafsat Suraj da aka fi sani da Chuchu, ta shaidawa kotun Majistri a Kano cewar ba ita ce ta hallaka abokin ta Nafi’u ba.
Da fari dai Hafsat ta shaidawa Yan sanda cewar ita ce ta kashe shi bayan ya hana ta kashe kan ta amma yau ta musanta hakan a gaban kotu.
Mai sharia kuma ta aike da ita kurkuku.
Wata matar aure, Hafsat Surajo da ake zargi da kashe abokin kasuwancinta, Nafiu Hafiz, ta musanta aikata laifin kisan kai da kuma yunkurin kashe kanta lokacin da aka gurfanar da ita a gaban kotu a yau Laraba.
Sai dai kuma duk da cewa Hafsat, wacce aka fi sani da Chuchu, a baya ta amsa laifin kisan, amma ta musanta tuhumar da ake mata a lokacin da ta bayyana a gaban wata babbar kotun majistare mai lamba 37 da ke Yankaba, Kano.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansanda a jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ta ce ana tuhumar mijinta Dayyabu Abdullahi da wani Malam Adamu da laifukan hada baki, boyewa da bayar da bayanan karya.
“A yau 27/12/23 Hafsat Surajo, kasancewar ta babbar wacce ake zargi, an tuhume ta da laifukan yunƙurin kashe kai da kuma kisan gilla wanda hukuncinsa na kisa ne, yayin da aka tuhumi mijinta Dayyabu Abdullahi da Mallam Adamu da laifukan haɗin kai, ɓoye. da Bada Bayanan Karya.
“Yayin da duk wadanda ake zargin su ka amsa laifukan su a wajen ƴansanda kan rawar da kowane ya taka a wajen aikata laifukan, a gaban babbar kotun majistre mai lamba 37 da ke ‘Yan Kaba Kan, lokacin da aka gurfanar da su, sai suka musanta aikata laifin,” in ji sanarwar.
0 Comments