Wata budurwa 'yar shekara 26 ta bindige saurayin ta har lahira


Wani dan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Cosmas Ugwu, ya mutu a sakamakon harbinsa da Budurwanda ta yi.

An kashe Ugwu ne a ranar Talata, 26 ga watan Disamba, ta hanyar budurwarsa mai shekaru 23, wacce aka bayyana sunanta da Amanda Uchechi Ugo, ‘yar asalin karamar hukumar Ahiazu Mbaise ta jihar Imo.

An ce jami’an da ke bakin aiki sun gudu ne bayan da suka ji karar harbe-harbe guda uku daga dakin da jami’in da ya rasu yake ciki.

An tattaro daga majiya mai tushe cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Dambe da ke yankin Ezinihitte.

Marigayin ya yi fada da budurwar tasa a dakin da ke ofishin ‘yan sanda, kuma ana cikin rikicin ne sai yarinyar ta kai hannu ta dauki bindigar marigayin, ta ja bindigar ta harbe shi har sau uku.

Post a Comment

0 Comments