MASHA ALLAH: Wani matashi dan Nijeriya ya kera keke mai tafiya akan ruwa - Abis fulani



Wani dan Najeriya mai suna Tari Ibruku ya kera keken zirga-zirga akan hanyoyin ruwa. 

Shafin NigerDelta Insider, da ya ruwaito labarin mutumin, ya ce Tari ya fito daga Twon-Brass a Kudancin Bayelsa kuma yana jin dadi idan aka kira shi da "Mu je zuwa."

Watanni hudu aka yi ana kera keken ruwan 

A cewar shafin na Facebook, Tari ya gwada keken ruwansa a wani kogi kwanakin baya kuma ya tabbatar da cewa yana aiki. 
Tari ya ce ya kwashe watanni hudu yana kera keken. 

Hotunan da NigerDelta Insider ya wallafa sun nuna Tari yana amfani da keken ruwa akan kogi.

Masu amfani da yanar gizo sun yabi Tari, yayin da suka kara masa kwarin guiwa. 

Jama'a na yabawa Tari Ibruku Amakson

Fab ya ce: "Ina tayaka murna dan uwa, ka ci gaba da aikin ka." 

Engr Onyebuchi Okafor ya ce: "Wannan babbar fasaha ce, ka ci gaba da yin aiki tukuru."

 Pst Henry Ebitimi ya ce: "Ina son in mallaki daya nan ba da jimawa ba, na taya shi murna."

Post a Comment

0 Comments