Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Allah yayiwa Tsohon shugaban kasuwar Kantin Kwari, Sharu rasuwa


Tsohon shugaban kungiyar ƴan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Sharif Sagiru ya rasu.

Ya rasu yana da shekaru 61 a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ya rasu ne a daren jiya Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.

Wata majiya ta shaidawa wannan jarida cewa marigayi Sharu ya halarci taro a gidansu a jiya Talata da rana kafin rasuwarsa da yamma.

Ya rasu yana da mata 2 da ‘ya’ya 13.

Tuni dai aka binne marigayin a makabartar Dandolo da ke Kano.

Comments

Popular posts from this blog