Wata mata ta baje kolin juna biyu da take dauke da shi sannan ta sanar da cewar ita da mijinta sun samu 'karuwa.
Kahboh Patience Fokong ta ce Allah ya azurta ta da mijinta da haihuwar diya macve.
Patience ta garzaya dandalin Facebook domin wallafa hotunanta a lokacin da take dauke da juna biyu, tana mai baje kolin yadda cikin ya amsheta.
A cikin hotunan, an gano ta tare da mijinta, Derrick, wanda ya kwantar da kanta a kan cikin nata.
Ma'auratan sun shiga daga ciki a farkon shekarar 2023, kuma Patience ta sanar da Legit cewa ta fuskanci kalubale da dama kafin auren.
Ta ce wasu daga cikin kawayenta basu goyi bayan ta auri mutum mai kankanta kamar mijinta ba, amma ta ce ta ji ta gani.
Ta ce:
"Kwarai na fuskanci kalubale da dama lokacin da mijina ya nuna aniyarsa na aurena.
Na fada ma iyayena, kuma duk basu yarda ba illa mahaifiyata, wacce ta kasance tare da ni sannan ta bukaci da na bi zuciyata. Kawayena suna ta yi mani ba'a, suna ta jikana da maganganu iri-iri haka wasu daga cikin dangi na."
Da zuwan diyarsu, Patience ta mika nasarar da ta samu wajen haihuwa ga Allah. Ta rubuta a Facebook:
"A karshen karshe, Allah ya yi mun da karfi. Ku tayamu yi wa lafiyayyiyar diyarmu maraba da zuwa cikin iyalinmu."
Nkubi ya ce:
Ina taya Patience da Derick murna mai tarin yawa. Allah ya albarkaci karamar gimbiyar cikin koshin lafiya ya raya ta."
Waah Bae ta ce:
"Allah ya rubanya ni'imar da ya yi maku. Sannu da zuwa yar diya."
Wata mata ta haihuwa a mota
A wani labarin, mun ji cewa wata mata mai juna biyu ta haifi wata jariri a cikin motar kasuwanci da ta nufi garin Warri a jihar Delta.
0 Comments