Rahotanni sun bayyana cewa hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya sanya wani katafaren jirgin samansa kirar Bombardier Global Express XRS a kasuwa don sayar da shi.
Ya biya dala miliyan 45.5 don mallakar jirgin mai zaman kansa a shekarar 2009 (shekaru 13 da suka gabata), lokacin da yake bikin cika shekaru 53 da haihuwa.
Shafin Billionaire.Africa ya ruwaito cewa, shugaban kamfanin simintin Dangote, ya yanke shawarar rage wasu daga cikin kadarorin alfarma da ya mallaka.
An kuma ruwaito Dangote na shirin sayar da jirgin ruwansa na alfarma da ya sanya miliyoyin daloli wajen mallakarsa.
Cikakken bayanai kan jirgin Dangote da zai siyar Nan da karamin lokaci ake sa ran mutane da kamfanoni za su fara gabatar da bukatar sayen jirgin saman, kirar Bombardier Global Express XRS, da aka yi wa farin fenti na Matterhorn, da shuɗi mai duhu, da ratsin jan zanen 'Peking', wadanda ke kawata gangar jikin jirgin, fuka fuki, da wutsiya.
Yana iya ɗaukar fasinjoji 14 zuwa 15 ba tare da takura ba, wannan wani jirgi ne da ya fi dacewa da attajiran da su ka mallaki biliyoyin naira.
Bangaren hagu na gaba na jirgin na dauke da kujerar zama da wurin hutawa ga ma'aikata, wanda aka kebe shi kawai don ma'aikatan jirgin a lokacin doguwar tafiya.
Binciken da Legit.ng ta yi a shafin intanet na Avbuyer, ya nuna cewa, ana sayar da irin wannan jirgin Bombardier Global Express XRS akan dala miliyan 18.5 (N14.85 biliyan).
Dangote Ya Tafka Asarar Naira Biliyan 525 A Cikin Sa'o'i 24 Kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta dauki wasu matakai da su ka kawo cikas ga kasuwancin attajiran kasar, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.
Kafin daukar wannan mataki, mafi yawan attajiran na cikin jerin masu kudi 500 a duniya, wanda Dangote ke jagorantarsu a Najeriya da kusan Dala biliyan 21, Legit ta tattaro.
0 Comments