Kamfanin MTN ya na bai wa kwastomomi damar cin bashi idan kudaden kirarsu ta kare yayin da suke bukatar kira.
Yayin da ya ke karin haske ga Legit, babban manajan hulda da jama’a na kamfanin, Fusho Aina ya tabbatar da lamarin. Har ila yau, Aina ya ce wannan matsalar na’ura ce ta jawo aka kwashe dukkan basukan da ake bin jama’a. Wane martani kamfanin MTN ya yi?
A cikin sanarwar da MTN ya fitar ta ce:
“MTN Najeriya ta tabbatar da matsalar na’ura yayin duba sauran kudade a wayoyin ku.
“A dalilin haka, wasu daga cikin kwastomomi sun samun sakon cewa an yafe musu basukan da ake binsu.
q“Da zarar an kamala shawo kan matsalar, basukan za su dawo, injiniyoyinmu suna kan gyara don shawo kan matsalar, muna baku hakuri.”
‘Yan Najeriya da dama sun yi farin ciki ganin yadda aka yafe musu basukan kafin daga bisani su shiga yanayi bayan sanarwar kamfanin.
0 Comments