Bauchi - A wani karatu da ya yi, Mansur Isa Yelwa ya yi tsokaci game da abubuwan da ke faruwa tsakanin kasashen Israila da Falasdinu.
Sheikh Mansur Isa Yelwa a darasin da ya gabatar kamar yadda aka wallafa a shafin Twitter, ya ce alamun rushewar Israila sun tabbata.
Hasashen Sheikh Ahmad Yasseen a kan Israila Malamin ya ce Marigayi Sheikh Ahmad Yasseen ya taba yin hasashen cewa kasar Israila za ta ruguje nan da shekarar 2047 bayan ta balaga.
Dole nan gaba kasar Israila za ta rugurguje Farfesan ya ce malamin ya taba fadawa Aljazeera a shekarar 1999 cewa daular Israila za ta cika wa’adin da Allah (SWT) ya yanke mata a duniya.
A ra’ayin Ahmad Yasseen, sai muzgunawar da Israila ta ke yi wa Falasdina ya yi kamari, sannan karfin kasar zai ragu, sai a daina labarinta.
Yayin da ta ke cikin ganiyarta, malamin ya ce abokiyar gabarsu za ta gawurta a duniya bayan da farko ba ta kai matsayin da ta ke kai ba.
Yadda Israila ta fara yin karfi a tarihi
"Abin da mu ka fahimta a Al-kur’ani, shekaru 40 ne kurewa na karfi. Duk wata kasa da za ta yi karfi, za ta yi shekaru 40 ne Daga nan kuma sai a samu wata da za ta gaje ta saboda Allah SWT bai yi alkawarin akwai wata kasa da za ta dawwama ba." - Sheikh Mansur Isa Yelwa esq. Daga 1947 zuwa 1987 Israila ta rika rarrafe, bayan nan ta fara mamaye Falasdina, daga 2027 kuma Sheikh Yasseen ya ce kasar za ta ruguje. Harin Hamas a kan Israila
A makon jiya aka samu rahoto da ya bada mamaki, kwatsam aka ji kungiyar Hamas mai rajin kare Falasɗinawa ta kai hare-hare a kan Isra'ila.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbayar da aukuwar harin da ba ta ta taba tsammani ba.
Comments
Post a Comment