Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Alkalin Kotun Daukaka Kara da ke jerin wadanda su ka samu karin girma jiya ya ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin mai suna Shagbaor Ikyegh ya rasu ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba ya na da shekaru 65 a duniya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalansa su ka fitar a yau Alhamis 7 ga watan Disamba a Makurdi babban birnin jihar Benue.
Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Makurdi da ke jihar amma ba ta bayyana dalilin mutuwar tashi ba, cewar TheCable.
Ikyegh na daga cikin alkalan da su ka samu karin girma zuwa Kotun Koli kuma zai yi ritaya ne a shekarar 2028, cewar TheNigeriaLawyer.
Comments
Post a Comment