Wata ƴar sanda mai suna Angela Adams a ranar Talata ta roki wata kotun gargajiya da ke zamanta a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, da ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta, Titus, kan rikicin cikin gida.
Ta fadi haka ne a cikin karar da ta shigar a gaban kotun game da mijinta.
“Mijina yakan yi min duka a duk lokacin da muka sami ƴar rashin fahimta. Yakan yi min duka kamar karamar yarinya.
“Koda yaushe idona ya ke nema idan yana duka na. Ko rannan ma da ya yi min duka, sai da ya kawo min naushi a fuskata, na yi sa’a na kare da hannuna amma duk da haka sai da naushin ya ji min rauni a hannu na,” in ji ta, lokacin da ta ke kuka.
Ta ce mijin nata ya karbi rancen kudi naira dubu 750,000 da sunan ta a wani banki.
“Lokacin da na tambaye shi me zai yi da kudin, sai ya gaya min cewa ya sayi katako ne da kwanon rufi daki da kudin, amma daga baya na ji cewa ashe wani gida ya kama haya ya gyara shi ya saka wata mace a ciki.”
Yaudara ta ya yi na aure shi, ban san ma ashe ya na da ‘ya’ya biyu ba, kuma kwanan nan ya yi wa wata ciki.”
“Ina rokon wannan kotu mai daraja da ta ba ni rikon dan daya tilo na wannan aure tare da raba auren kafin mijina ya kashe ni kuma ba za a samu wanda zai kula da yaro na ba”.
Wanda ake kara,Titus wanda shi ma dansanda ne, bai halarci zaman kotun ba.
Sai dai mai shari’a Thelma Baba, ta bayar da umarnin a kai karar wanda ake kara ta hannun lauyansa, sannan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, domin jin ta bakin wanda ake kara da kuma kare kansa.
Comments
Post a Comment