KE DUNIYA: Ta Kashe Yaran Kishiyarta Dan Kwana Hudu Da Haihuwa Ta Hanyar Ba’da Masa Guba..


Wata matar aure mai shekaru 24 mai suna, Furera Abubakar dake zama a kauyen Bantu a karamar hukumar Ningi, jihar Bauchi, ta fada komar ‘yan sanda bayan ta kashe yaron kishiyarta dan kwana hudu da haihuwa, wanda ko sunansa ba a yi ba.

A jawabin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakli, da Rariya ta samu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa an haifi yaron a ranar 15 ga wata, aka kuma kashe shi a ranar 19 ga Agusta, 2023.

Ana zargin matar ta sakawa jaririn guba ne ya mutu.

Post a Comment

0 Comments