Ana cikin matsin rayuwa, wani mai sana'ar tura baro ya tsere da shinkafa rabin buhu mallakin wata mata a yankin Kwali dake babban birnin tarayya, Abuja.
Lamarin ya afku ne kasa da mako guda bayan wani 'dan achaba ya tsere da buhun garin masara a yankin Abaji da ke birnin tarayyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Yadda mai baro ya tsere da kayan abinci a kasuwar Kwali Matar da aka sacewa shinkafar mai suna Talatu Yakubu, wacce ta sanar da mutane faruwar lamarin a kasuwar Kwali a ranar Litinin, ta ce ta dauki mai baron ne domin ya tayata fitar da shinkafar da kayan miya zuwa bakin hanya.
Acewarta, ta zo kasuwar ne sannan ta siya shinkafa mudu 30 da jakar Semovita da kayan miya gabannin bikin 'diyarta da za a yi a ranar Juma'a a kauyen Sheda.
Ta ce ta tsaya siyan kayan attarugu da timatir ne kusa da kofar fita kasuwar lokacin da mai baron ya yi batan dabo.
0 Comments