Mai girma tsohon shugaban kasa ya Gwangwaje Dattijon Da Sabuwar Mota kirar GOLF 3, Da Kuma Buhun Shinkafa 5, Da Kuma Wasu Kudade.
Hausaloaded ya samu tattara martanin mutane a karashin wannan rubutu suna cewa.
@Hussaini s Maigana ga abinda yake cewa:
Suma mutane da jarabarsu ,mutuminnan yace baya so a rinqa ziyartarsa .
Amma saboda rashin zuciya nawasunmu Sai sunje.
Kar a manta fa har alkaba’i yake Neman jawo Mana saboda masu ziyartarsa.
@Abubakar sadeeq tajadden yana cewa :
Wallahi kullum burina Allah ya nuna man ranan da zanyi ido biyu da general muhammadu buhari. Allah ya qarawa baba buhari lafiya, da nisan kwana
Allah ya tsare Mana gabanshi da bayanshi alfarmar fiyayyen halitta muhammurrasulillah SAW.
@saifullahee Ibn sallau yana mai cewa :
Wato Baba Dai Har Yanxu Yana Nan Akan Bakar Shi Baya Son Cima Zaune, Shiyasa Ya Gwangwaje Dattijo Da Golf 3 Don Ya Dunga Fita Neman Na Magi, Allah Ya Saka Da Alkhairy Baba Manjo.
@Ibrahim Alhaji shehu cewa yake ;
Yawwa, haka akeyiwa masoyi, Amma mutane sana ta nuna soyayyar su gareka Amma baba sai kayi burus dasu, idan anyi magana kace Kai bakasata,to baba kasani tunda har kazama shugaban kasa agurun wasu fa kayi Sata duk da dai mu Muna da kyakykyawan zaton bakayiba. Kuma duk abun daka ba masoyinka baka biyashiba.muna Maka fatan alkhairi.
0 Comments