Al’ummar kauyen Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa sun shiga rudani bayan aurar da wata yarinya ‘yar shekara 4 ga wani dattijo.
Iyayen yarinyar ne suka ba da auren yarinyar wacce ba a bayyana sunanta ba ga dattijo dan shekara 54 wanda hakan ya jawo cece-kuce a yankin.
Yaushe aka daura auren yarinyar?
Dattijon mai suna Akpos ya auri yarinyar a ranar 26 ga watan Disamba inda masu rajin kare hakkin kananan yara suka yi Allah wadai da auren.
Kungiyar ta bayyana auren a matsayin babban laifi da kuma cin zarafi inda ta ce hakan ya sabawa kndin tsarin mulki, cewar Tribune.
Iyayen yarinyar sun tabbatar da cewa dattijon shi ne mijin yarinyar tun a baya kafin rayuwa inda aka kwatanta wannar al’ada da abin takaici.
Wata majiya a kauyen ta bayyana cewa yarinyar ta ce dattijon shi ne mijinta tun a rayuwarsu ta farko wanda ya mutu shekaru aru-aru.
Yarinyar ta kara da cewa ta yi ta yawo wurare daban-daban don neman mijinta amma ba ta same shi ba.
Martani kungiya kan auren
Majiyar ta ce:
“Yarinyar ta ce idan har ba a barta ta auri mijin ba, ba ta da wani abin yi a kauyen Akeddei inda ta ce za ta mutu cikin aminci.
“Don gudun kada a rasa yarinyar, iyalan sun yanke shawarar bayar da yarinyar da yin kasaitaccen biki don kara hada masoyan da suka dade da juna.”
Shugaban Gidauniyar DO reshen jihar Bayelsa, Elvis Mannie ya tabbatar da faruwar lamarin, cewar Newstral.
Mannie ya ce Gidauniyar ta fara binciken lamarin don tabbatar da ceto yarinyar daga wannan iftila’i da ta shiga.
0 Comments