Duk da ana samun wasu iyayen suke zabawa ‘ya’yansu mata mazan da zasu aura, sai dai mafiya yawan iyaye suke baiwa ‘ya’yan nasu damar zaban wanda suke so su aura da kansu. Wannan kuma shi abunda musulunci ya aminta da shi saboda gudun kada ayiwa yarinya auren da bata so.
Sai dai kuma duk da irin daman da iyayen suke baiwa ‘ya’yan nasu na zabin wanda suke so da kansu, iyaye basu damu su daura yaran nasu akan wani ma’aunin da zasu tabbatar da mijin daya dace dasu ba kamin su gabatar da shi ko bashi damar turo iyayensa. Mafiya yawan iyaye muddin ‘yarsu tace ta samu wanda zata aura abunda suka fi damuwa da su sani shine idan tana son shi da gaske. Wanda tabbatar da hakan shikenan a wajen su ta samu miji tunda dai itace tace tana sonsa.
Wannan matakine ko sakacine da iyayen da suka maida soyayya zalla ya zama shine abun auna mijin da ‘yarsu zata aura.
Da yake ita kuma wacce ake son babu wani tsani da aka daurata akai na alamun mijin da zata aura, duk wanda ya zo mata da iya magana, kwalliya ko kudi shi kenan a wajenta ta samu mijin aure.
KALLI CIKAKKEN BIDIYONN πππ
Comments
Post a Comment