Wani mutumi ya shiga hannun ‘yan sandan Najeriya saboda yadda ya matsawa wata mata a hanya.
Kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano ya sanar a Facebook, matar ta shigar da kara a ofishinsu.
Kin Iya Kunu?
Da ya dame ta da tambayar "Kin Iya Kunu?", ita kuma sai ta shigar da kararsa a ofishin ‘yan sanda da ke kusa.
A sanarwar da ya fitar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wannan mutumi yana tsare a bayan kantarsu a halin yanzu.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan ya fadi wannan labari ne domin ya zama darasi ga masu irin wannan hali.
Matar ta iya kunu ko kuwa?
Da wani ya nemi jin ko wannan mata ta iya kunun, sai Abdullahi Kiyawa ya fada masa zai iya zuwa ya bincika
Gwarzon jami'in tsaron bai fadi matakin da aka dauka ba a kan wannan mutumi.
A cewar kakakin dakarun ‘yan sandan reshen Kano, matar za ta dawo ofishin Anti Daba da ke unguwar Tal’udu.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matar ta na tafiyarta a gefen titi sai mutumin ya rika bin ta yana addabar ta.
BAKI SHIKE YANKA WUYA
"Ya ga wata Baiwar Allah tana tafiya a gefen titi, ya bita yana ta ce mata, "Kin Iya Kunu", har ya fusata ta, taje ta shigar da korafi a Ofishin 'Ƴan Sanda.
Yanzu haka wannan matashin yana tsare a bayan
"Counter".
Gani ga wane ..." - Abdullahi Haruna Kiyawa.
0 Comments