Wani dan kasuwa mai suna Nasiru Yunusa ya yiwa matarsa Aisha Hamisu tayin sakin auren da ba a saba gani ba: ta biya shi naira miliyan daya sannan ta yi tafiyar ta.
Ma’auratan, wadanda suka yi aure a karkashin tsarin shari’ar Musulunci a shekarar 2021, kuma iyayen ‘yar watanni 13, suna gaban kotun Upper Area dake Kubwa, FCT, kan neman kashe auren.
Bukatar Nasiru kafin ya saki matarsa Aisha ce ta shigar da karar inda ta nemi kotu ta raba auren saboda wulakancin da Nasiru ya ke yi mata, inda ta ce ya kore ta da 'yarsu daga gidan shi a watan Afrelu 2022.
Sai dai Nasiru ya amince da yin sulhu da matar ma damar za ta biya sa naira miliyan daya da ya kashe kan shari'ar, da kuma wasu kudi da ya kashe a zaman kotun, Leadership ta ruwaito.
Ya ce idan har ta biya kudin to zai ba ta takardar saki, yana mai shaidawa kotun cewa:
"Ina da hujjoji da suka nuna na kashe naira miliyan daya ta dalilinta
Aisha ta yi martani kan bukatar mijinta Amma a nata bayanin, Aisha ta ce sam ba ta da wani sauran muradi na Nasiru, kuma tsawon zamanta a gidan iyayenta bai taba tallafa mata da kudi ba, hatta haihuwar 'yarsu ita ta yi komai.
"Domin kawo karshen aurenmu, zan biya shi naira 50,000 kudin sadakin da ya biya na aure na, amma banda wannan, babu wasu kudi da zan iya ba shi." A cewar ta game da bukatar Nasiru na biyansa naira miliyan daya.
The Guardian ta ruwaito Mai shari'a Mohammed Wakili ya dage sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Janairu, inda ake sa ran za a sake kallon wata diramar kan bukatar Nasiru.
Kotu ta yanke hukunci kan matashin da ya cinna wa mahaifiyarsa wuta Mai shari'a a wata kotun jihar Niger ya ba da umurnin rataye wani matashi da aka kama da laifin kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta a jihar.
0 Comments