Mai shari'a Hakeem Oshodi na babbar kotu a Ikeja, Lagas, ya yi gagarumin gargadi ga jama'a.
Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, Oshodi ya yi gargadin cewa ya kamata mutane su daina ajiye masa layu a cikin kotunsa.
Ya yi wannan gargadin ne a yayin shari’ar wasu mutane biyar da ake tuhuma da laifin kisan wani Ifeanyi Etunmuse, a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba.
"Kada wanda ya bar layu a cikin kotuna. Kada a sake maimaitawa. An tsinci wani laya bayan dage zaman karshe a shari'ar kisan kai."
Da yake nuni ga layan a matsayin kaya, ya ce "Kada ku bar kayanku a nan kuma. Baya aiki kuma," rahoton The Nation.
Mutane biyar da ake tuhuma; Atunrase Omolabi, Shittu Olawale, Olaide Opeifa, Olanrewaju Adebiyi wanda aka fi sani da Maja, da Jamiu Omosanya wanda aka fi sani da Orobo, an tuhume su da laifin yunkurin kisan kai da kisan Etunmuse a Western Funeral Home, Ijede Ikorodu.
Comments
Post a Comment