Fitaccen darakta kuma jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood, Aminu S Bono, ya riga mu gidan gaskiya.
Abokin aikinsa kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ne ya tabbatar da rasuwar Daraktan a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
El-mustapha ya kuma yi wa marigayin addu'ar samun rahamar Allah, inda ya yi fatan Allah ya sa Aljanna ta kasance makomarsa.
A sanarwan da ya wallafa a shafinsa yau Litinin, 20 ga watan Nuwamba, 2023, Abba El-Mustapha ya ce: "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa shahararren darakta a Masana’antarmu ta Kannywood, Aminu S Bono rasuwa."
"Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kura-kuransa, ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani."
Ƙarin bayani na nan tafe...
0 Comments