Ƙasar Amurka ta fitar da sanarwar gaggawa ga ƴan ƙasarta dake Najeriya su yi taka tsan-tsan da shiga manyan otel domin akwai “babbar barazana ta kai hari” a manyan otal dake “manyan biranen Najeriya”
Sanarwar ta ce hukumomin tsaron Najeriya na kokarin dakile wannan barazana.
Wakiliya ta ruwaito an umurci ‘yan kasar Amurka su rika sanya ido a manyan otal-otal da za su kama, su rika lura da duk wajen da suke, sannan su riƙa tuntubar sashin shawarwari tafiye-tafiye kafin su kama otal a Najeriya
Sanarwar ta kara da cewa “Gwamnatin Amurka tana sane da sahihan bayanan da ke nuna cewa akwai babbar barazana ga manyan otal-otal a cikin manyan biranen Najeriya.”
“Amma hukumomin tsaron Najeriya na aiki tukuru domin dakile wannan barazana.
“Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci ‘yan Amurka da su yi la’akari da wannan bayanin lokacin da suke shirya masauki ko ziyartar manyan otal a Najeriya.”
0 Comments