Bidiyo: “Daga yau mun karya farashin kayanmu da kashi 50 buhun Siminti 1800 Sugar 20k Fulawa 19k—BUA


Fitaccen attajirin ɗan kasuwar Afrika Abdussamad BUA ya mayarwa da Dangote zazzafan martani, sannan ya ce daga yau ya karya farashin illahirin kayan da kamfanoninsa ke sarrafawa da kashu 50% cikin ɗari tare da ƙalubalatar Dangote da cewa shima idan ya isa kuma ya cika ɗan kishin ƙasa to yayi irin abinda yayi na karya farashin kayansa Abdussamad ya ƙara da cewar 

"Kamfani na na BUA ya ɗauko tarihi tun daga shekarar 1991 lokacin da aka yi wahalar Sukari, amma sai aka yi sa’a mu muna da Sukarin a ƙasa, kuma Aliko Dangote ya nemi in saida masa sukarin, don ya siyar da tsada na ƙiya sai a karshe lamarin ya ƙare a Kotu, a haka na jajirce cikin watanni ukku har ila yau, kuma na taɓa karban aron fili daga Usman Dantata don in kafa kamfanin Siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin

Saboda haka a halin yanzu na bada umarnin a riƙa siyar da ko wane buhun Siminti a kan Naira 1,800 buhun Sugar kuma Naira 20,000 Fulawa ₦19,000 Shinkafa ₦28,000 Taliya ₦4,000" In ji shi kamar yadda ya bayyana a firarsa da manema labarai

Kunji fa muna fatan Allah ya ƙara ɗaukaka wannan bawa nashi, don Allah ana buƙatar kowa yayi masa addu'ar fatan alheri kuma a taimaka wajen tura wannan labarin na farin ciki zuwa sauran groups don ƴan'uwa Musulmi su ƙara yi masa addu'a Allah ya cika masa burinsa ya kuma bada ikon aiwatar da wannan ƙuduri na alheri.

Post a Comment

0 Comments