Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Wani Sabon Hari a Taraba


Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga da ake zargin mayaƙan wata ƙabila ne sun kai hari kasuwar Didango da ke ƙaramar hukumar Karim-Lamido a jihar Taraba. Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a kasuwar sun salwantar da rayukan mutum biyu. 

Hakazalika an jikkata mutane da dama tare da kwashe kayayyakin miliyoyin naira yayin harin. 

Wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya shaida wa Daily Trust a wata hira ta wayar tarho cewa ƴan bindigan dauke da muggan makamai sun kai hari garin ne a ranar Laraba, wacce ta kasance ranar kasuwa da misalin ƙarfe 9:00 na dare. 

"Maharan sun fito ne daga wani kauye da ke kusa da mu. Babu wanda ya tunzura su saboda al'ummar Digango waɗanda galibinsu ƴan kabilar Wurkum, Jarawa da Hausa-Fulani ne ba su da wata takaddama da kauyen da maharan suka fito da har za su kawo mana wannan harin." 

Sai dai Adamu ya ce matasan garin sun dakile harin inda aka tilastawa ƴan bindigan tserewa zuwa kauyensu wanda ke da nisan kilomita huɗu daga Didango. Wani mazaunin garin Bello Dauda ya bayyana cewa harin da ƴan bindigan suka kai wani yunkuri ne na sake haifar da sabon rikicin ƙabilanci a yankin. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ce mutum ɗaya ne ya mutu sannan wasu biyar suka samu raunika. 

Ya ce an kama mutane biyu da ake zargi da kai harin, inda ya ce suna taimakawa ƴan sanda wajen gano wadanda suka kitsa kai harin.

Comments

Popular posts from this blog

An karrama mutumin da bai taba shiga aji ba da matakin digiri (Dr) Bayan ya kirkiri risho mai amfani da ruwa Tareda janareto - Abis Fulani News

Ina Mazan Da Matan Suke?___Sabon Sirri Gareku Mata Da Maza Kalli Yadda Zaku......

Gaba ta koma baya : Ni wallahi Jaki nake son aure – murja kunya