Wasu ƴan bindiga a yammacin ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, sun sake yin garkuwa da wasu ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar Channels tv. A cewar shaidar ganau ba jiyau ba, ɗaliban guda biyu waɗanda namiji da mace ne, an sace su a ɗakin kwanan ɗaliban da ke kusa da jami'ar da misalin karfe 9:00 na daren ranar Asabar a unguwar Sabon Garin Damba da ke Gusau, babban birnin jihar. Mazauna yankin sun ce ƴan bindigan sun farmaki unguwar ne ƴan mintuna kaɗan bayan karfe 8:00 na dare inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi domin tsorata mazauna yankin. Wane ƙoƙari jami'an tsaro suka yi? Jami’an tsaro sun yi ta musayar wuta da ƴan ta'addan a ƙoƙarin fatattakarsu, amma ƴan ta'addan sun tafi da ɗalibai guda biyu. Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya bayyana cewa jami'an tsaro na haɗin gwiwar ƴan sanda da sojoji, sun bi sahun ƴan ta'addan. Kokarin yin magana da ...
Comments
Post a Comment