Wata Amarya tayi shiru tana kallon mahaifiyarta tana rawa cikin nishadi da mijinta a lokacin ɗaurin aurensu.
A cikin faifan bidiyon da shafin Official Wife TV ya sanya a TikTok, angon ya riƙe ƙugun surukarsa yayin da suke ta tiƙar rawa a wajen taron.
Da alama amaryar ta ji cewa an mayar da ita saniyar ware, saboda ɓacin rai ya lullube fuskarta yayin da take kallon abin da ke faruwa.
Tabbas matar ta so ta yi rawa da mijinta, amma angon ya nuna yana jin daɗin da rawa da surukarsa.
Rawar da angon ya yi da surukarsa ta haifar da ce-ce-ku-ce A wasu lokutan a cikin faifan bidiyon, amaryar ta riƙa sunkuyar da kanta ƙasa a wata alama da ke nuna cewa ba ta jin daɗin abin da ke faruwa.
Masu amfani da shafukan sada zumunta da suka ga bidiyon sun ce abin da angon ya yi bai dace ba.
Bidiyon ya yaɗu sosai a yanar gizo, inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu a kai.
Ga kaɗan daga ciki:
@richardyorm ya rubuta:
"Wannan auren yana cikin HADARI!!!"
@Tirimud3 Hemaa ya rubuta:
"Amaryar ba ta jin daɗi ko kaɗan."
@Mrs.Swann ta rubuta:
"Mahaifiyar amaryar ta ce,
"Ba na son zaman lafiya, ina son matsaloli."
0 Comments