Yan Sanda Jihar Kano Sun Kama Jaruma Amal Umar Sun Tura Ta Kotu Akan Zargin Tayi Yinkurin Basu Cin Hanci




Rundunar ƴan sanda shiyya ta daya Zone One, dake jihar Kano, ƙarƙashin AIG Umar Mamman Sanda ta gurfanar da jarumar Kannywood Amal Umar a gaban kotun majistiri mai lamba 24 dake unguwar gyadi-gyadi a birnin Kano.


Wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan CSP Bashir Muhammad ya fitar, ta ce an gurfanar da Amal Umar a gaban kotun ne bisa zargin ta da yunƙurin bawa wani ‘dansanda cin-hancin kuɗi Naira Dubu Ɗari biyar.


Acewar binciken ‘yan sandan, Amal Umar ta fara ne da baiwa ɗan sandan da ke bincike a kan wani laifi da ake zarginta da hannun wajan aikatawa naira dubu dari biyu da hamsin (250,000).

Post a Comment

0 Comments