Kotu takes hukunta kamfani a Amurka da ya tilastawa ma'aikacinsa aske gemu




Kotu ta ci tarar wani kamfanin Amurka, Blackwell Security Services Inc., dala dubu 70 saboda ya nemi wani ma'aikaci Musulmi ya aske gemu.

Hukumar tabbatar da daidaito wajen daukar aiki ta Amurka (EEOC) ta shigar da karar kamfanin bisa tuhumar karya dokar daukar aiki da hakkin ma'aikata.

Hukumar EEOC ta zargi kamfanin da kin karbar tsarin addinin ma'aikacin, tare da tilasta shi zabar aikinsa ko addininsa, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin ya nemi ma'aikacin ya zabi addini ko aikinsa A cewar EEOC, ma'aikacin na da ikon tafiyar da rayuwarsa bisa tafarkin addinin da ya ke ciki ba tare da wata wariya ba.

An ruwaito cewa kamfanin Blackwell ya nemi mutumin ya sake gemunsa ma damar yana son yin aiki a kamfanin.

Lokacin da ya nemi a bashi damar barin gemunsa saboda addini, sau kamfanin ya ce zai sallame shi ma damar ba zai aske ba.

Kotu ta ci tarar kamfani saboda karya dokar sashe na VII Hukumar ta ce ma'aikacin ya aske gemun nasa ba da son ransa ba, sai don gudun kar ya rasa aikin.

Ta ce wannan laifi ya saba da sashe na VII na dokar 'yancin dan Adam ta 1964, wacce ta haramta nuna bambanci kan addini tsakani ma'aikaci da inda yake aiki.





Post a Comment

0 Comments