Hukumar hisba ta cafke mota makare da kwalabe dubu 24 na barasa - a Jihar Kano



Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata babbar mota makare da kwalaben barasa fiye da dubu 24 da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri da tsakar dare.

Babban daraktan hukumar, Alhaji Abba Sufi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin da yake duba motar da aka kwace a hanyar Zariya a daren ranar Talata.

Yadda Hisbah ta kama mota makare da kwalaban giya Ya yi nuni da cewa jami’an Hisbah a jihar sun zage damtse wajen aiwatar da dokar hana fasa kwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a jihar, The Punch ta ruwaito.

A cewar Sufi: "An kama motar dake dauke da sama da kwalabe dubu 24 na barasa daga hannun masu fasa kwauri a hanyar Zaria da tsakar dare." 

Shugaban hukumar ya yabawa jami’an Hisbah bisa hadin kai da suka yi da masu ruwa da tsaki a yaki da safarar barasa a jihar, kan matsayar da jihar ta dauka na bin tsarin shari’a.

A nasa jawabin, mukaddashin kwamandan sashen kwararru kan manyan laifuka na hukumar, Fu’ad Dorayi, ya ce an kama direban motar da wasu mutum biyu. 

Dorayi ya godewa jami'an rundunar na Dawakin Kudu, inda ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wata mota da ke dauke da kayayyakin da ake zargin na laifi ne. 

Hanyoyin da masu fasa kwaurin ke amfani da su sun hada da titin Kano/Zaria, titin Kano-Gwarzo-Dayi, titin Kano-Katsina, titin Kano-Maiduguri, da titin Kano-Hadejiya. 

Bidiyon yadda aka kama motar Wani ma'abocin shafin X, mai suna Arewa guy, @Arewa_guy ya wallafa bidiyon yadda hukumar ta kama motar giyar.

Post a Comment

0 Comments