Kakakin rundunar jihar SP Ahmed Mohammad Wakil ya ce budurwar ta nemi kudin daga hannun saurayin bayan wata bukata da ta biya masa, shi kuma ya hana ta.
A ranar Laraba ne 'yan sanda suka kama matashin, bayan da ya caka wa budurwar wuka a kahon zuci a wani dakin da ta kama a 'Bayan Gari', inda mutane su ka jiyo ihunta suka kai dauki.
Matashin ya amsa laifinsa, za a gurfanar da shi gaban koliya
A kokarin jama'a na balle kofar dakin, matashin ya caka wa wani Zaharaddeen Adamu wuka a hannu, amma dai mutane suka fara nada wa matashin na jaki, rahoton Daily Trust.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce jami'an atisayen wanzar da zaman lafiya sun je 'Bayan Gari' inda suka ceci matashin daga hannun fusatattun jama'ar, tare da daukar gawar budurwar.
Wakil ya ce: "Bayan tuhumar Ibrahim, ya amsa laifin kashe budurwar, inda ya bayyana cewa ya hadu da ita a Facebook kuma sun sha soyayya har ya saci kudin mahaifinsa ya je Fatakwal don su gana."
Jami'in dan sandan ya ce an gano wuka a hannun matashin, yayin da rundunar ke ci gaba da bincike inda za ta gurfanar da shi gaban koliya nan ba da jimawa ba.
Sufetan 'yan sanda ya kashe kansa bayan bindige abokin aikinsa
A wani labarin, wani Sufeto a rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa dan sandan mai suna Sufeto Nelson Abuante ya harbe abokin aikinsa a ranar Lahadi a Nyogor-Lueku da ke karamar hukumar Khana a jihar.
0 Comments