Wata 'yar Nigeria ta zama babban Kwamishina a kasar Amurka - Abis_fulani


An nada Dokta Olusimbo Ige, ƴar Nijeriya a matsayin kwamishiniyar Sashen Kiwon Lafiyar Al’umma ta Chicago, inda ta zama bakar fata ta farko da ta taba samun irin wannan matsayi.

Hon. Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar kula da ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, NIDCOM, ce ta bayyana hakan a cikin sakon taya murna da ta aike mata.

A cikin sanarwar taya murnar, Dabiri-Erewa ta bayyana ci gaban Ige a matsayin “babban lamari”, ta na mai cewa: “Ta kafa tarihi! Taya murna ga bakar fata ta farko a cikin Tarihin Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Al’umma ta Chicago da aka nada a matsayin Kwamishina.”

A cewar wata sanarwa daga Abdur-Rahman Balogun, mai magana da yawun NiDCOM, Dabiri-Erewa ta ce nadin Ige ya sake tabbatar da cewa ƴan Najeriya mazauna kasashen waje suna yin fice da kuma tasiri mai kyau a duk inda suka samu kansu.

Shugabar ta NIDCOM ta bukaci Ige da ta cika abin da ake bukata tare da zaburar da sauran kwararrun matasan Najeriya suma su zama jakadu nagari a kasar a ayyukan da suka zaba.

Nadin na Dokta Ige ya biyo bayan amincewar magajin garin Brandon Johnson ne biyo bayan korar Dr Allison Arwady, tsohon kwamishina a Sashen Kiwon Lafiyar Al’umma na Chicago a Amurka.

Post a Comment

0 Comments