"Baya ta koma gaba": Rigima ta barke bayan matashi ya dage sai auri budurwarsa mai ciki



Wata mata ta bayyana yadda ba zato ba tsammani aka ɗage wani ɗaurin aure bayan cin amanar da amaryar ta yi.

A cewar wata mata mai suna @HRH_onyx akan manhajar X, cikin amaryar ba na angon da za ta aura ba ne.

Cikin da amarya ta yi ya kawo cece-kuce 

Wannan lamarin ya haifar da tashin hankali na rashin tabbas kuma ya haifar da tambayoyi game da makomar dangantakarsu.

Duk da haka, duk da yanayin, angon yana tunanin cigaba da bikin, shawarar da ta fuskanci adawa mai ƙarfi daga danginsa. Rashin amincewar dangin ya ƙara daɗa wani nau'i na rikitarwa ga yanayin da ya riga ya kasance mai sarƙaƙiya, inda masoyan biyu suka rasa abin yi.

Mai ba da labarin ta rubuta akan X: "An dakatar da bikin auren da ya kamata a yi saboda matar tana da cikin wata ɗaya, kuma cikin ba daga angon da za ta aura ba ne, saboda angon ya tafi yawon shaƙatawa. Mutumin ya ce yana son cigaba da bikin. Ƴan uwansa sun ce a'a."

Masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyinsu sosai kan lamarin. 

@loshantii ya rubuta: "Dalilin da ya sa yake son cigaba shi kaɗai ya sani. 

Ba ruwansa da soyayya. 

Yana da mugun nufi."

@Anigboson ya rubuta: "Ban gane mutumin ba. 

Me yasa kake son ɗaukar nauyin ciki wanda ba naka ba? 

Ƴan uwansa su tsaya tsayin daka. Mu, surukai na X, muna goyon bayansu sosai." 

@Mareeyah_ ta rubuta: "Wataƙila yana so ya cigaba da hukunta ta. Wasu mazan haka suke." 

@IamEkene_ ya rubuta: "Mutumin ya duba duk abin da ya kashe kuma baya son ya yi asara, shi ne kawai dalilin da ya sa yake son komai ya cigaba, ko kuma yana sonta sosai kuma bai damu ba, me na sani?" 

Amarya Ta Soke Bikinta 

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata amarya ta soke bikin aurenta da angonta ana saura sati ɗaya biki.

Amaryar dai ta soke bikin auren ne saboda angonta ya ce ba shi da kuɗin da zai biya domin ɗaukar nauyin raƙashewa a bikin. 

Post a Comment

0 Comments