Matar ta wallafa sakon wata ƴar Amurka Ɗaya daga cikin sakonnin neman mazan auren ya fito daga wata mace ƴar shekara 31 a duniya daga ƙasar Amurka, tana neman mijin aure na gaske ba zancen wasa ba.
Wannan ya sa masu amfani da kafar sada zumuntan suka fara nuna sha'awarsu na neman abokan zama daga wasu ƙasashe, hakan ya kara ma labarin armashi.
Wani saƙon da ya ƙara jan hankali shi ne na wasu Musulmai maza guda biyu da ke neman a sama musu haɗi a ƙasar da suke rayuwa watau Burtaniya.
Olaa ta wallafa a shafinta cewa: "Na faɗa muku shekarar nan ba zata fita kuna gwauraye ba, wannan kyakkyawar budurwar yar shekara 31 a ƙasar Amurka ta tura mun sakon neman mijin aure."
"Tana son mijin ya kasance ɗan Amurka ko Kanada.
Wasu musulmai biyu da ke zama a Burtaniya suna son a sama musu haɗi a nan ƙasar.
Haka wani kirista ya nemi a haɗa shi da wata a Burtaniya."
Martanin mutane kan bukatar ƴar Amurka
@LarryXcell ya ce:
"Tana son mijin ya zama ɗan ƙasar Amurka ko Kanada, lallai bata shirya aure ba."
@massive_Edafe ya ce:
"Watau dai ba ta bukatar ɗan Najeriya kenan."
@laurentdarl ya ce:
"Ni ma har yanzun gwauro ne."
@Dex2ro ya ce:
"Ko zan iya shiga cikin maneman ba'amurkiya yar shekara 31?"
0 Comments