Al’ummar Fulani mazauna yankin Ogunmakin a jihar Ogun sun shiga cikin rudani da a ranar Litinin da ta gabata, yayin da wasu abokai guda biyu, Abdullahi Audu da Usman Muhammed suka kusa kashe junansu sakamakon sabani da suka samu kanlemun kwalba.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Audu wanda aka ce shi ne ya fara wannan rikicin, ya zaro adda tare da datse hannun Muhammad a lokacin fadan.
Ganin an datse hannunsa gaba daya, shi ma Muhammed ya zaro wuka ya soke cikin Audu, abin da ake kyautata zaton ramuwar gayya ce kafin mutane su shiga tsakanin su.
Sai dai lamarin ya kara yin muni a lokacin da wukar da Muhammed ya soka wa Audu a ciki ta fito da 'yan hanjin Audu, lamarin da ya kwantar da su gaba daya rai a hannun Allah.
Ganin rikicin da ya barke tsakanin abokanan biyu, sarkin fulanin yankin, Alhaji Wakili, ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Owode Egba domin kai rahoton faruwar lamarin.
Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa a halin yanzu dukkan wadanda abin ya shafa suna karbar magani a wani asibitin da ke garin.
Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Omolola Odutola, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce sun fara gudanar da bincike.
“Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, muna kan bincike,” Odutola ta bayyana hakan a wani sakon WhatsApp a ranar Talata.
Comments
Post a Comment