Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Fadar shugaban kasa ta sanar a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, cewa kasar Faransa za ta dawo da dala miliyan 150 da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ya sace.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna jin dadinsa ga matakin da Faransa ta dauka yayin ganawarsa da ministar harkokin Turai da harkokin wajen Faransa Catherine Colonna.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar/
Najeriya da Faransa, inda ya bayyana irin ci gaban da aka samu tun ziyarar da ya kai birnin Paris bayan hawansa mulki.
Ya jaddada muhimmancin inganta hadin gwiwa a harkokin siyasa da tattalin arziki tare da maraba da hadin gwiwarsu kan sauyin yanayi, hadewar tattalin arziki, ilimi, da al'adu.
Ya ce:
“Na gode da albishir kan dawo da kudin da Abacha ya sace. Muna godiya da hadin kanku game da dawo da kudaden Najeriya.
Za a yi amfani da su yadda ya kamata wajen cimma manufofin ci gabanmu."
0 Comments