"Dangote da BUA" Sun Dawo da Rikicinsu Sabo, Ana Tono Abin da ya Faru Tun 1991 - Abis Fulani


Kamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a ranar Juma’ar nan, a matsayin martani ga zargin da kamfanin 

Dangote Group ya jefe sa da shi. A wasikar da ta fitar ga duniya, BUA Group ya karyata takwaransa watau Dangote, an dade Abdul Samad Rabiu ya na ta gwabzawa da faru-tun-1991

Silar rikicin BUA da Dangote a Najeriya 

Kamfanin na BUA ya dauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar sukari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabiu ya na da sukari a kasa. 

BUA ya ce Aliko Dangote ya nemi a saida masa sukarin, sai a karshe lamarin ya kare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabiu ya jajirce na watanni uku. 

Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin. 

A dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karbi aro daga hannun kawun na Dangote. 

BUA: Wahalar shiga siminti bayan sukari 

Premium Times da ta wallafa wasikar ta ce sai bayan shekara Rabiu ya iya komawa harkar sukari, yanzu kamfaninsa ya zarce kowa a yammacin Afrika. 

Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam kalubalen nan ba su iya taka masu burki ba. 

Martanin da kamfanin Dangote ya yi wa BUA 

Amma a wani rahoto da Daily Nigerian ta fitar a dazu, an ji kamfanin Dangote ya karyata zargin badakalar kudin waje, ya ja kunnen masu yin sharri. 

Kamfanin Dangote Industries Limited ya karyata zargin cewa Jim Obazee ya na bincikensa kan abubuwan da su ka faru lokacin Mr. Godwin Emefiele.

Post a Comment

0 Comments