Da alama akwai aiki a gaban hukumar Hisbah ta jihar Kano domin Murja Ibrahim Kunya ta nuna ba ta da niyyar yin aure.
A wani bidiyo da mu ka ci karo da shi a dandalin Facebook, Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewa bakaken aljanu su ka hana ta aure.
Dr. Muhammad Hashim Sulaiman ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa a safiyar Laraba.
Murja Kunya da maganar aure Wannan Baiwar Allah da ta shahara a kafar Tik Tok ta ankarar da manemanta cewa idan aka zo mata da batun aure, ta na gwabje mutane.
"Ni fa na fahimci mutanen nan so su ke yi su aurar da ni, kuma babu wani kure-mure, wallahi aljanu ne a jiki na. Manya-manyan bakaken aljanu ne.
Ni ma ni kadai wani lokaci sai in hau naushe-naushe, ko ku ga ina fizge-fizge." - Murja Ibrahim Kunya Murja Kunya ta na gwabje manema Murja Kunya ta ce abin na ta ya fi kamari ne a cikin dare, a sanadiyyar haka ne wani maneminta da ya zo zance, ya yabawa aya zakinta.
A cewarta, tun da wannan ta’aliki ya yi subutar baki ya fada mata ya na kaunar ta, da ta yi masa wani kutufo, sai dai aka gano shi a wani jeji.
A bidiyon, an ji Murja Kunya ta na cewa watakila aljanun tsohon masoyinta ne su ka dawo jikinta bayan rasuwarsa, su ke neman hana ta aure.
"Da ka yi mani zancen aure sai kutufo, amma duk wanda ya ga zai diba a haka, babu damuwa ka diba, amma ka tabbatar kai ‘dan dambe ne. Haka na ke kuma ni ma ban san ina kai harin ba, sai idan na gama ragargazar mutum na ke sani.
Haka kurum duka na ke yi, ina kuma ga a ce an makure ni da karfi da yaji, an cusa a dakin miji?"
- Murja Ibrahim Kunya
An yi wa Murja Kunya duka?
Kwanaki aka yi ta yawo da labari cewa wasu matasa da ba a san ko su wanene ba sun yi wa jarumar ta TikTok dukan tsiya a garin Kano.
Ana zargin matasan da su ka yi wannan zalunci sun sauyawa Murja kamanni.
An yi kira ga jami’an tsaro su yi bincike domin a hukunta su.
0 Comments