Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin kudade a kasar.
Bankin ya bayyana haka ne ta bakin daraktan yada labarai, Isa AbdulMumin a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da korafin karancin kudade a kasar, cewar Punch.
Har ila yau, bankin ya musanta cewa akwai karancin kudin inda ya ce akwai makudan kudade da za su isa juya harkar kasuwanci.
Sanarwar ta ce:
"Saboda gudun kokwanto, mu na da isassun kudade da za a yi harkokin kasuwanci da su.
"Mu na sanar da ku cewa duk wani kudi da aka ba ku halastacce ne, bai kamata ku ki karba ba."
0 Comments