ALLAHU AKBAR; Allah yayi ma Mai kula da kabarin Manzon Allah ya rasu - Abis fulani


Allah Ya yi wa mutumin da ke kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, rasuwa.

Agha Abdou Ali Idris Sheikh, daya ne daga cikin mutanen da suka fi dadewa suna hidima a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.

Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami ta sanar cewa, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar Litinin.

An gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Manzon Allah sannan aka kai shi makwancinsa na karshe.

Abdou Ali Idris Sheikh shi ne Agha na uku da ya rasu cikin shekaru 10 da suka wuce.

A baya yawan masu aikin Agha ya haura mutum dubu daya, amma a halin yanzu wadanda suka rage a raye ba su fi biyar.
Aminiya

Post a Comment

0 Comments