Yanzu - Yanzun: 'Yan bindiga sun sace daliban jami'a da dama a jihar Nasarawa


Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai huɗu na jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare. 

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa 'yan bindigan sun sace ɗaliban da misalin ƙarfe 10:30 na dare lokacin da suka kai farmaki Anguwan Ka'are, ƙaramar hukumar Keffi. 


Ɗaliban da maharan suka yi garkuwa da su sun haɗa da, Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel, da kuma Goodness Samuel, duk 'yan aji ɗaya watau 100 Level. 

Ya ce jami’an tsaron cikin jami'ar jihar Nasarawa na aiki ƙafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya. 

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka? 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin ga Channels tv ta wayar tarho ranar Talata. 

Ya ce da sanyin safiyar ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wani gida a Angwan Ka'are. 

“Hukumar 'yan sanda ta samu labari da misalin karfe 12:55 na safe, bayan wani kiran gaggawa cewa yan bindiga sun kutsa wani gida da ke Angwan Ka'are, Keffi sun sace mutane." 

"Dakarun 'yan sanda da haɗin guiwar jami'an sojoji sun kai ɗauki inda suka kewaye Anguwar, amma bisa rashin sa a ba su tarad da maharan ba." “Kwamishanan ‘yan sanda ya bada da umarnin farautar maharan da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba.” 

Post a Comment

0 Comments