Gwamnatin Abba Ta Sanya Ranar Ɗaura Auren Yan Mata da Zawarawa - Abis Fulani


Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa kawo yanzu an kammala dukkan wasu shirye-shiryen gagarumin ɗaura auren nan da ta kudiri aniyar yi a faɗin jihar. 

Sakamakon haka gwamnatin ta sanya ranar Jumu'a, 13 ga watan Oktoba, 2023 a matsayin ranar ƙulla auren ma'aurata 1,800 da ta ɗauki nauyi daga sassan ƙananan hukumomi 44.

Ɗaura auren wanda ake kira da 'Auren Zawarawa" ya kunshi samari da 'yan mata da zawarawa maza da mata kuma gwamnatin Kano ke ɗaukar nauyin komai, Dailytrust ta ruwaito. 

Gwamna ya ziyarci hedkwatar Hisbah Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ne ya sanar da haka yayin da ya kai ziyara hukumar Hisbah domin duba shirye-shiryen da aka yi. 

Ya kuma nuna jin dadinsa da irin shirye-shiryen da aka yi a kasa kawo yanzu, ya kuma yabawa hukumar Hisbah da ma’aikatar lafiya bisa yadda suka gudanar da ayyukan da aka dora musu. Gwamnan ya kuma nuna farin cikinsa ganin yadda shirin ya ƙunshi marasa galihu da kuma masu naƙasa. 

Post a Comment

0 Comments