Fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata, ya yi rashin ɗaya daga cikin jikokinsa, Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata.
Batulu ta rasu tana shekaru 40 a duniya bayan ta sha fama da jinyar ciwon sikila na tsawon lokaci, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Marigayya Batulu ta kammala karatunta na zama lauya watau Law kafin Allah ya karɓi rayuwarta. Ta rasu ta bar mahaifiyarta, Hajiya Ummul Khair Aminu Dantata.
Mahaifiyar mamaciyar ita ce ɗiya ta farko ga Alhaji Aminu Ɗantata.
Haka kuma Batulu ta rasu ta bar mahaifinta, Alhaji Baba Alhassan Ahmad Dantata.
Yaushe za a mata jana'iza?
Za a yi wa marigayya Batulu sallar jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Masallacin Jumu'a na Koki da ke cikin kwaryar birnin Kano da misalin ƙarfe 10:00 da safiyar yau Talata. Idan baku manta ba, Alhaji Aminu Ɗantata, ya rasa matarsa, Hajiya Rabi, wacce Allah ya mata rasuwa a watan Afrilun wannan shekara da muke ciki 2023.
0 Comments