“Sai Kace a Karkara”: Matashiya Yar Najeriya Ta Baje Kolin Boyayyun Wuri a Turai


Wani bidiyo mai tsuma zuciya na fafutukar wata yar Najeriya da ta je neman gida a Birtaniya ya dauka hankalin masu amfani da soshiyal midiya da dama. 

Ta nadi bidiyon tafiyarta zuwa wajen duba wani gida da ta gani a soshiyal midiya, amma sai gwiwowinta suka sace da abun da ta gani a zahiri. 

Ta kuma nuna banbanci tsakanin hadaddun hotuna na Birtaniya da ta gani a yanar gizo da kuma unguwanni masu datti da kazanta da ta ci karo da su a hanyarta ta zuwa ganin gidan. 
Ta nuna rashin gamsuwarta da gidan, tana mai cewa ya yi nisa sosai daga tashar jirgin kasa mafi kusa kuma cewa ba za ta ji dadin tafiya ita kadai a cikin duhu ba bayan ta sauka daga jirgin kasan. 

Bidiyon nata wani karin haske ne na zahirin gaskiya da ban dariya game da kalubalen da ke tattare da samun gidan haya da ya dace a wata kasa. 

Post a Comment

0 Comments