Rundunar sojin Isra’ila ta ce, adadin mutanenta dake hannun Hamas ya karu zuwa 310 - Abis Fulani

Rundunar sojin Isra’ila a ranar Juma’a ta ce adadin sojojin Isra’ila ya karu zuwa 310 tun bayan fadan da ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba da kungiyoyin Falasdinu a Gaza.

A wani taron manema labarai Daniel Hagari mai magana da yawun rundunar ya ce an sanar da iyalan sojojin game da mutuwar ‘yan uwansu. Ya ce Isra’ilawa 233 ne kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza, wanda ya kara adadin daga 228 da aka sanar a baya. Kakakin sojin Isra’ila ya kara da cewa har yanzu adadin bai kare ba yayin da sojoji ke ci gaba da gudanar da bincike kan sabbin bayanai.

Al-Qassam Brigades, reshen kungiyar Hamas da ke dauke da makamai, a cikin wata sanarwa da ta fitar a baya, ta ce tana tsare da mutane kimanin 200-250 da suka hada da sojojin Isra’ila da fararen hula. Hagari ya kuma ce sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, tare da mayar da hankali a daren jiya a gabashin Gaza.

A safiyar ranar Juma’a ne dai sojojin kasar Isra’ila suka kai wani takaitaccen kutse a kusa da unguwar Shuja’iyya wanda ke zama hari na biyu na kasa tun ranar 7 ga watan Oktoba. Jami’an sojin Isra’ila, a lokuta da dama, sun tabbatar da shirye-shiryen sojojin na gudanar da wani gagarumin farmaki ta kasa a Gaza, amma suna jiran haske daga shugabannin siyasar Isra’ila.

Rikicin Gaza ya fara ne a lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kaddamar da Operation Al-Aqsa – wani harin ba zato mai ban mamaki a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya hada da harba makaman roka da kuma kutsawa cikin Isra’ila ta kasa, ruwa da iska. Hamas ta ce kutsen na a matsayin ramuwar gayya ne kan harin da aka kai a Masallacin Al-Aqsa da kuma karuwar cin zarafi da matsugunan Isra’ila ke yi kan Falasdinawa. Daga nan ne sojojin Isra’ila suka kaddamar da ruwan bama-bamai a kan yankunan Hamas da ke zirin Gaza. Kusan mutane 8,500 ne aka kashe a rikicin da suka hada da Falasdinawa akalla 7,028 da kuma ‘yan Isra’ila 1,400.

Post a Comment

0 Comments