Babbar Kotun yanki mai zama a Kubwa a birnin tarayya Abuja ta datse igiyoyin auren da ke tsakankn Hafsat Abdullahi da mijinta, Adesegun Rufai.
Kotun ta raba ma'auratan waɗan da suka shafe shekaru huɗu suna tare da juna saboda matar ta daina ƙaunar mijinta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Alkalin Kotun mai shari'a Muhammad Wakili ya raba auren ne ta hanyar "Kul'i" kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan matar ta roƙi a raba su saboda ta daina sha'awar zama da shi.
Sai dai magidancin bai bayyana a gaban Kotun ba duk da an aika masa da takardar sammaci bayan matarsa ta shigar da ƙarar neman saki.
Duk da haka mai shari'a Wakili ya rushe auren da ke tsakaninsu karkashin oda ta 9, doka ta 3 na kundin dokokin Kotun yanki, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Bayan haka ya umarci Hafsat ta fara iddah na tsawon watanni uku da kwanaki 10 kamar yadda shari'ar addinin Musulunci ta tanada kafin ta sake yin wani auren. Ƙarar ta matar ta kai Kotu kan mijinta Tun da farko, Hafsat ta shaida wa alkalin Kotun cewa ta auri mijinta ne a shekarar 2019 kamar yadda Addinin Musulunci ya shar'anta kuma babu wata matsala.
Matar ta ƙara da cewa a halin yanzu ba ta da sha’awar auren, don haka ta roki kotu da ta raba auren saboda rashin soyayya da rashin jituwar da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.
0 Comments