Wani ɗan Najeriya ya ba da labarin yadda ya yi asarar gidansa mai ɗakuna uku a Lugbe, cikin babban birnin tarayya Abuja.
A kullum tsohuwar budurwar tasa tana nuna masa rashin gamsuwa da unguwar, wanda hakan ya sanya shi yanke shawarar sayar da gidan don faranta mata rai.
Matashi ya sadaukar da gidansa don soyayya A cikin nuna soyayya da neman sasanci, mutumin wanda yake amfani da sunan @JasonNotJerulo akan shafin X, ya sadaukar da gidansa saboda soyayyar su.
Abin takaici, duk da sadaukarwar da ya yi, soyayyar ta su ta zo ƙarshe.
Sakamakon haka Jason ya tsinci kansa ba gida a Abuja, inda ya yi nadamar sayar da kadarorinsa.
Rashin gidan nasa ya sa ya yi ta tunani a kan yadda soyayya ka iya sanya mutum ya yi abin da baya da niyya, da illar fifita abin da wani ke so fiye da wanda mutum yake so.
A kalamansa: "Lokacin da nake zaune a Abuja ina da gida mai daƙuna uku da ke Lugbe.
Tsohuwar budurwa ta sai ta riƙa ƙorafi akan wurin har na sayar da gidan don faranta mata rai. Yanzu mun rabu kuma ba ni da gida a Abuja.
Wani lokaci soyayya wani makamin sanya ka yin abin da baka yi niyya ba ne.”
Masu amfani da yanar gizo sun mayar da martani Da jin labarin Jason, masu amfani da yanar gizo sun bayyana mamakinsu kan shawarar da ya yanke.
Mutane da yawa sun ɗauke hakan a matsayin sakarci wanda ruɗin soyayya ya ja masa.
@Wizebaba ya rubuta: "Kowace soyayya tana buƙatar lokaci, kawai ka ba ta lokaci."
@ThisisEazee ya rubuta: "Kai daga mai gida zuwa mai haya saboda TOTO?? Shin Genevieve ce ita??"
@Sarauniya ta rubuta: "A matsayina na mace na rantse maka Wallahi. Ka yi abun kunya."
@Irunnia_ ya rubuta: "Bari na yarda cewa wannan wasa ne. Ba kowa ba ne zai yi wannan wawancin ba."
@47kasz ya rubuta: "Dole ne wannan ya kasance wasa.. ba zai yiwu ka zama sakarai haka ba."
@talk2veee ta rubuta: "Kada ka yarda mace ta ɗora ka akan hanyar rashin nasara.
Idan ba ta sonka a yadda kake, gaya mata ta ba ka lokaci ko ta amince da kai a haka. Duk tsiya dai abin da za ta yi daga ƙarshe shi ne ta rabu da kai."
0 Comments