Kwankwaso butulune matsoraci, mum kusa binne siyasara a Kano - Dan Bilki Kwamanda ya magantu





Wani sojan baka a siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da dadewa ba za su kawo karshen siyasar jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso. 

Kwamanda ya ce yayi mamakin yadda har Tinubu ya tsorata da Kwankwaso, wanda a cewar sa shi Kwankwaso 'duba gari ne' wanda bai kamata aji tsoron sa ba.


Legit Hausa ta ci karo da tattaunawar da aka yi da mai fashin baki kan harkokin siyasar jihar, a wani bidiyo da aka wallafa a shafin @danbalkicommander a TikTok.


Kwamanda ya ce yanzu suka fara adawa da Kwankwaso A cikin bidiyon, wanda kuma wani Enjiniya Alkassim Fge ya wallafa a shafinsa na Twitter, an ji Dan Bilki Kwamanda na cewa: 

"Yanzu muka fara adawa da gwamnatin Kano, kuma babu wanda ya isa ya hana mu kalubalance su tun daga kan shi wannan Rabiu Kwankwason. 

"Ai Rabiu Kwankwaso butulu ne a siyasa, har na yi mamakin yadda aka tsorata Bola Tinubu da Kwankwaso. Matsoraci ne a siyasa mara kunya."

Kwamanda ya ci gaba da cewa: "In Allah ya yarda sai mun binne siyasar Kwankwso da shi da 'yan korensa, kuma zai dandana kudarsa a hannun su Kwamanda."

Akwai mutane masu mutunci a jam'iyyar NNPP - Kwamanda Mai fashin bakin ya kuma ce yanzu ne Rabiu Kwankwaso zai fara ganin adawa a wajen su, kuma ba sa shakkar kowa a jam'iyyar NNPP.

Sai dai ya ce akwai mutanen kirki a jam'iyyar, wadanda suke biyayya don karbo dukiyarsu da suka kashe, ba wai don suna son jagoran jam'iyyar ba. 

Ya yi ikirarin cewa: "Idan kana neman butulu a siyasa ka hadu da Rabiu Kwankwaso to magana ta kare, don haka babu abin burgewa a yi alfahari da dan siyasa irinsa." 

Kalli bidiyon a kasa:




Post a Comment

0 Comments