'Yar 419 ce: Wani Matashi ya koka bayan budurwa ta cinye 20k da ya aika mata na mota - Abis_fulani


Wani mutumi da ya turawa budurwa kudin N20,000 domin ta yi kudin motar zuwa ganinsa a Abuja ya nuna fushinsa saboda ta ki zuwa.

A wata wallafa da ta yi a TikTok, an jiyo muryar mnutumin yana kiran budurwar a matsayin yar 419.

Mutumin ya ce lallai sai dai yarinyar ta yi kokarin daina dabi'arta na karbar kudi daga wajen maza sannan ta ki kai masu ziyara.

Sai dai kuma budurwar mai suna Nancy a TikTok, ta dage cewa kudin ya yi kadan kuma ba za ta iya zuwa Abuja da shi ba.

Bata bayyana inda take ba amma dai ta bayyana a sashin sharhi cewa kamata ya yi ace mutumin ya yankar mata tikitin jirgin sama. 

Ta rubuta: "Ta yaya zan yi amfani da 20k kan kudin motar zuwa ganin namiji? 

Har zuwa Abuja? 

Asiri ne wannan? Ba su shirya ba har sai sun yanki tikitin jirgin sama." 

Kalli wallafarta a kasa: 
@ukhaylove4 How i wan take use 20k for transport go see man?all the way to Abuja?😂😂💔 na juju be that? #fyp #viral ♬ original sound - user17736938751

Post a Comment

0 Comments