Ya kamata farashin litar man fetur yakai 750 - cewar Babban Bankin Duniya


Bankin duniya yana ganin akwai alamar tambaya game da farashin litar fetur duk da gwamnati ta ce ta cire hannunta.

Ranar Laraba The Nation ta rahoto masanan bankin suna nuna cewa da alama har gobe gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin mai.

Babban masanin bankin na Duniya ya halarci taron da aka yi a Abuja, ya ce ya kamata a rika saida duk litar man fetur ne kan N750. 

Mista Alex Sienaert yake cewa idan aka duba farashin Dalar Amurka a kan Naira, za a fahimci lallai litar fetur ta kai N750 yau a kasuwa.

Sienaert yana zargin an dawo da tallafin fetur 

“Idan mu ka kiyasta abin da ya kamata ya zama shi ne farashin man fetur, kuma mu ka yi lissafin cewa ana shigo da kaya ne a kan farashin canjin gwamnati, za a ga kamar kudin fetur bai yi daidai da farashin yanayin kasuwa ba, hakan ya nuna an dawo da wani bangaren tallafi.

Muna tunani ya kamata fetur ya zama N750, fiye da N650 da ‘yan Najeriya su ke biya.” - 

Alex Sienaert Babu shakka fetur ya wuce N650 Vanguard ta ce ba dole ba ne farashin ya tabbata kamar yadda Sienaert ya fada, a cewarsa kiyasi ne kurum da ya tabbatar da lita ta fi N650.

Bankin Duniya ya gamsu cewa shakka babu gwamnati ta cire hannunta wajen canjin kudi wanda hakan ya shafi farashin shigo da mai.

Ana kuka da tsadar fetur

Wani rahotonmu ya nuna mafi yawan al'ummar Najeriya su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa da tashin kudin fetur.

Cire tallafin man fetur da aka yi ya jawo farashin fetur ya karu zuwa kusan N700 sannan kudin gas da ake saye domin yin girki ya tashi. 

Post a Comment

0 Comments